Jami'an 'yan sanda da jandarmomi da ke Bangiu, babban birnin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR, sun dawo da sintirin da suka saba yi, bayan wata ganawa da aka yi a yammacin ranar Alhamis da sojojin kasar Faransa da kuma shugaban rikon kwaryar kasar Michel Djotodia.
Bayanai na cewa, an dakatar da sintirin ne ranar Talata, sakamakon karuwar zaman dar-dar, bayan da aka kashe sojojin kasar Faransa guda biyu, yayin musayar wuta da 'yan tawaye a lokacin da sojojin na Faransa ke kokarin aiwatar da shirin kwace makamai daga hannun tsoffin 'yan tawayen Seleka da ke mulkin kasar a halin yanzu.
Ko da yake bayan ziyarar da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya kai birnin Bangui, an yanke shawarar barin 'yan sanda da jandarmomin kasar, su ci gaba da sintirin da suka saba gudanarwa na yau da kullum.
Ana kuma fatan shirin kwace makaman ya hada da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai, ciki har da masu adawa da Balaka.
An tura sojojin kasar Faransa zuwa jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ce, domin su tallafawa dakarun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa da ke kasar (MISCA) wajen maido da doka da oda a kasar da ake fuskantar tashin hankali tun lokacin da Djotodia ya kama mulki a ranar 24 ga watan Maris din shekarar 2013. (Ibrahim)