in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi na kwashe mutanenta daga Afrika ta Tsakiya
2013-12-23 10:41:03 cri

Gwamnatin kasar Chadi ta dauki niyyar kwashe mutanenta dake cikin mawuyacin hali a kasar Afrika ta Tsakiya, tare da kafa wani shirin karbar mutanen a kasarta tare da ba su kulawa yadda ya kamata, in ji faraminstan kasar Chadi Kalzeube Pahimi Deubet a ranar Lahadi a cikin wata hirarsa tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Dukkan matakan da suka wajaba, an dauke su domin kare mutanenmu, da dukiyoyinsu a kasar Afrika ta Tsakiya, in ji mista Kalzeube Pahimi Deubet.

Yan Chadi 200 da yawancin kananan yara, mata da tsoffi daga Bangui na CAR sun sauka a filin jiragen sama na Hassan Djamouss dake N'Djamena, babban birnin kasar Chadi a ranar Lahadi. Haka ma a ranar Asabar, kusan mutane 354, aka kwashe daga kasar Afrika ta Tsakiya. A yanzu haka, daruruwan 'yan kasar Chadi da dama ke zaman jiran kwashewa a filin jiragen saman M'Poko dake Bangui. Tun yau da 'yan makonni ne, 'yan kasar Chadi mabiya addinin musulunci, da sojojin kasar Chadi dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya (MISCA) suke fuskantar barazana da hare-hare daga sojojin sa kai na kasar Afrika ta Tsikiya mabiya addinin krista da aka fi sani da "Anti-Balaka" suna zargin 'yan kasar Chadi da hada kai da tsoffin 'yan tawayen Seleka wajen habarar shugaba Francois Bozize a cikin watan Febrairun shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China