Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana rashin jin dadinsa, don gane da halin rashin tabbas da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR ke ciki.
Ban ya ce, cikin wannan shekara dake daf da karewa, Afirka ta Tsakiya na dada tsundima cikin wani irin yanayi maras kyau, wanda ke iya munana halin rarrabuwar kai tsakanin al'ummun kasar da ake fama da shi.
Babban magatakardar MDDr ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake karbar rahoton bana, dake kunshe da yadda al'amura ka wakana a fadin duniya. Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin rikon kwaryar kasar, da ta tabbatar da tsaron rayukan al'umma. Har ila yau, ya yi kira ga jagororin addinai da su kaucewa daukar dukkanin wasu matakai da ka iya rura wutar rikici.
Fadace-fadace dai sun sake ta'azzara ne cikin watan Maris, bayan da 'yan tawayen Seleka suka hambarar da gwamnatin shugaba Francois Bozize. A hannu guda kuma gwamnatin rikon kwaryar kasar mai ci karkashin firaminista Nicolas Tiangaye, na ci gaba da fuskantar tarin kalubalen shawo kan dauki ba dadi, da kungiyar Seleka da takwararta ta mabiya addinin kirista ke yi a sassan kasar. (Saminu)