Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika AU ya bayyana matukar damuwarsa kan tabarbarewar yanayi a kasar Afrika ta Tsakiya CAR, musamman kan tashen-tashen hankali na baya bayan nan da suka faru a Bangui, babban birnin kasar da barkewar rikicin addini da na kabilu.
A yayin zaman taronsa karo na 40 na ranar Jumm'ar da ta gabata a Addis Abeba, kwamitin ya dauki niyyar ba da umurnin kara yawan sojojin wucin gadi na tawagar kasa da kasa dake kasar Afrika ta Tsakiya (MISCA) zuwa 6000, wannan zai sanya tattauna wa'adin a cikin watanni uku, bisa la'akari da sauye-sauyen da za'a samu kan halin da ake ciki da kuma bukatu a wurin da kuma bisa tushen rahoton da shugabar kwamitin AU za ta gabatar.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ya jaddada yin allawadai kan cin zafarin bil adama kan fararen hula, har da ayyukan kisa, sace mutane, kama jama'a da tsare su ba bisa doka ba, azabatar da mutane, fyade da kuma shigo da kananan yara cikin rundunar soja. (Maman Ada)