Sanarwar ta kuma yi kira ga bangarorin mabanbanta dake kasar, da su dakatar da rura wutar rikici, su kuma rungumi shawarwari a matsayin hanyar warware rikicin dake addabar kasar.
Bisa rahoton baya bayan nan da ya fito daga ofishin kakakin MDDr, an ce a ranar 19 ga wata, an kai wani hari sansanin rundunar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu, harin da ya haddasa mutuwar fararen hula a kalla 11. Sabanin mutane 20 da a baya aka ce sun rasu sakamakon farmakin. (Maryam)