Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan 19 ga wata ya ce, ya damu matuka game da cigaba da tashin hankali da ke faruwa a wassu sassan kasar Sudan ta Kudu, inda ake take hakkin bil adama tare da kisan mutane babu gaira babu dalili, abin da ke kara rura wutar rikici.
Ofishin majalissar dake Sudan ta Kudu yana iyakacin kokarinsa na ganin ya ba da kariya ga fararen hula tare da ma'aikatan majalissar da sauran kungiyoyin ba da agaji na kasashen waje dake kasar, a cewar Mr. Ban cikin wata sanarwa da kakakin majalissar ya fitar da sunan shi.
Fiye da mutane 30,000 suka nemi mafaka a sansanonin majalissar dake Sudan ta Kudu saboda fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye, inda aka ba da rahoton samun mutuwar mutane a daya daga cikin sansanonin, kamar yadda wani babban jami'in majalissar ya tabbatar a ranar Alhamis din nan yana mai alkawarin yin duk abin da ya kamata na ba da kariya ga jama'a dake cikin hadari.
An kai wa daya daga cikin sansanonin majalissar dake Akobo a yankin Jonglei da ake tashin hankali hari kuma akwai rahoton samun mutuwar mutane, amma ba'a tabbatar da adadinsu ba, in ji mataimakin magatakardar majalissar Jan Eliasson lokacin da ya zanta da manema labarai, yana mai tabbatar da cewa, tattaunawa a siyasance ita ce kadai hanya mafita ta hana yaduwar wannan tashin hankali. (Fatimah)