in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Somaliya sun sauke firaministan kasar
2013-12-03 09:55:00 cri

A ranar Litinin din nan 2 ga wata, majalisar dokokin kasar Somaliya suka jefa kuri'ar amincewa, inda suka sauke firaministan kasar Abdi Farah Shirdon.

Shugaban kasar Hassan Sheik Mohamoud tun da farko sai da ya yi kira ga Shirdon da ya sauka daga mukaminsa bisa zargin gwamnatinsa da rashin dacewa da kuma gazawa wajen cika alkawuran da ya dauka.

Sakamakon kwanaki biyu da aka shafe, ana muhawara da tattaunawa a kan bukatar da aka gabatar ta kuri'ar rashin tabbaci a majalisar, 'yan majalisu 250 cikin 275 sun kada kuri'ar sauke shi a zaman da suka yi na wannan rana na Litinin.

Kusan 'yan majalisu 184 sun jefa kuri'a ta nuna amincewa da wannan bukata ta rashin tabbaci a kan shi, guda 66 kuma ba su amince ba, don haka masu rinjaye suka amince kamar yadda kakakin majalisar Mohammed Osman Jawari ya sanar bayan jefa kuri'ar.

Abdi Farah Shirdon ya zauna a kan mukaminsa na tsawon watanni 15 tun bayan zaben shugaban kasar Hassan Sheik Mohammed a watan Oktoba na shekarar bara.

Dan shekaru 55, tsohon 'dan kasuwa kuma masanin tattalin arziki ya yi ta kare bayanai na gwamnatinsa, inda ya ce, ya cika alkawuran da ya dauka tare da yin alkawarin bin shawarar da majalisar dokokin suka dauka a kan shi.

Shugaban kasar ta Somaliya yana da kwanaki 30 na sake nada sabon firaminista wanda shi kuma zai nada sabuwar gwamnati. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China