in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Somaliya ya sha alwashin cigaba da yakan 'yan kungiyar Al-Shabaab
2013-11-21 14:12:59 cri

Firaministan Somaliya Abdi Farah Shirdon a jiya Laraba 20 ga wata ya ce, gwamnatinsa za ta inganta kokarin da take yi wajen yaki da kungiyar Al-Shabaab, rana daya bayan da kungiyar ta kai mummunan hari a tsakiyar kasar dake kahon Afrika.

Firaministan ya sha wannan alwashin ne lokacin da ya ziyarci wadanda wannan harin ya shafa kuma suke kwance a asibitin cibiyar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika da MDD AMISOM a Mogadishu, babban birnin kasar.

Ya ce, gwamnatin kasarsa da tawagar AMISOM za su cigaba da yakan kungiyar, har sai an ga an murkushe su gaba daya daga kasar Somaliya.

Fiye da mutane 20 ne suka hallaka, da dama kuma suka ji rauni, a ciki, sun hada da 'yan sandan kasar, bayan da wani 'dan kunar bakin wake ya tuko wata mota dauke da bam ya afka wa ginin hukumar 'yan sanda a garin Beledweyne mai nisan kilomita 300 daga arewacin Mogadishu, babban birnin kasar.

Wannan ne dai hari na biyu da kungiyar ta kai a garin Beledweyne a cikin wata daya, kuma wannan gari shi ne sansanin ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar na AMISOM daga Djibouti. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China