Hong Lei ya ce, Sin ta yaba matuka da ra'ayin kasashen biyu da kokarin da kasa da kasa suka yi, musamman ma kungiyar AU kan wannan batu,ta kuma yi fatan kasashen biyu za su yi amfani da wannan dama domin kyautata tare da bunkasa dangantaka tsakaninsu zuwa gaba.
A yayin da yake amsa tambayar manema labarai dangane da kokarin da Sin ta yi domin kyautata dangantaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, Hong Lei ya ce, a matsayin aminiyar kasashen biyu, Sin ta tsaya tsayin daka wajen sa kaimi ga yin shawarwari tsakaninsu domin daidaita matsaloli iri iri.
A cewar sa tun daga watan Yuni na bana zuwa yanzu, manzon musamman na shugaban Sudan ta Kudu, da ministan harkokin waje na Sudan sun kawo ziyara a Sin, yayin da wakilin musamman na gwamnatin Sin kan batun kasashen Afirka ya kai ziyara a yankin da kasashen biyu ke ciki har sau uku. Shi ya sa Sin ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Haka kuma ya ce Sin na fatan yin kokari tare da sauran kasashen duniya, domin kara ba da taimako wajen sa kaimi ga kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.(Fatima)