in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar Sudan ta Kudu ta zo kasar Sin don halartar baje-koli
2013-10-19 16:50:21 cri
Yanzu haka, 'yan kasuwar kasar Sudan ta Kudu fiye da 100 suna birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, don halartar gagarumin bikin baje-kolin kayayyaki kirar kasar Sin.

Wannan tawaga, wadda ta kunshi kwararru a fannonin aikin banki, da gine-gine, da na'urorin aikin jinya, da na sashen mai da iskar gas, da na aikin tsabtace ruwa, da wutar lantarki, da dai sauransu, za kuma ta tattauna da wakilan kamfanonin kasar Sin daban daban.

Makasudin ziyarar 'yan kasuwar a wannan lokaci dai shi ne, karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2, musamman ma a bangarorin tattalin arziki, da kasuwanci, da harkokin zuba jari, da musayar fasahohi tsakanin al'ummun kasashen Biyu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China