A cikin wata sanarwa da kakakinsa ya bayar a birnin Entebbe na kasar Uganda inda babban magatakardar yanzu haka yake ziyarar aiki,yace zai ci gaba da bin sahun wannan tattaunawa kuma a shirye yake yayi duk abinda ya kamata don ganin wannan kokarin da kasar Sin ke son yi ya samu karbuwa.
A lokacin ganawar a nan Beijing Shugaba Xi ya jaddada matsayin da Sin ta dauka na ganin an kau da makaman nukiliya a zirin Koriya, yana mai cewa ya kamata wannan aniya dukkannin bangarorin da abin ya shafa su tabbatar da ganin ta samu karbuwa a ko wane irin yanayi kuwa hakan zai kawo.
Kau da makaman nikiliya da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya wani buri ne da al'ummomin wurin ke son ganin ya tabbata a yankin, inji Mr Xi.
A nashi bangaren manzo na musamman Choe Ryong Hae wanda ya isar da wasikar Shugaba Kim Jong Un a lokacin ganawar sa da Shugaba Xi,ya ce wannan burine na hakika da kasar Jamhuriyar demokradiya na koriya ke fatan ganin an cimma domin samar da zaman lafiya a yankin, a samu inganta tattalin arziki da kuma rayuwar al'umma.
A cewar shi Kasar DPRK a shirye take ta yi aiki da bangarorin da abin ya shafa domin warware dukkan matsalolin da ya shafi hakan ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna da suka hada da tattaunawa da kasashe shida, sannan kuma kasar sa tana da aniyar rungumar duk wani shawara da aka bayar da zai kiyaye zaman lafiya da karko a zirin koriya. (Fatimah Jibril)