in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na nuna damuwa game da rushe majalisar ministoci da shugaban kasar Sudan ta kudu ya yi
2013-07-25 15:28:49 cri

A daren ranar 23 ga wata agogon Sudan ta kudu, shugaban kasar Salva Kiir ya tsige mataimakinsa Riek Machar daga mukaminsa ba zato ba tsamani, ya kuma bayyana rushe majalisar ministoci, mai mambobi 29. Bayan samun labarin, lamarin ya baiwa al'ummar kasar mamaki, tare da jawo damuwar kasashen duniya kan yadda matakin zai shafi makomar kasar Sudan ta kudu da ta fi karancin shekaru a duniya.

Wannan labarin ya fito ne daga gidan talibijin na kasar Sudan ta kudu a daren ranar Talatan da ta gabata. A sa'i daya kuma, shugaba Kiir ya sanar da cewa, za a rage yawan hukumomin gwamnati daga 29 zuwa 18, amma bai ambaci wadanda matakin zai shafa ba. Yanzu mataimakan ministoci ne ke shugabantar hukumomin na 'dan lokaci. Gwamnatin kasar ba ta bayyana dallilan da suka sanya shugabanta ya dauki wadannan matakai ba, sai dai ya dage cewa, gwamnatin za ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata har zuwa lokacin da aka nada sabbin ministoci.

Babban wakilin kasar Sudan ta kudu mai kula da shawarwari tsakanin kasar da makwabciyarta Sudan, Pagan Amum, shi ma yana daga cikin jerin wadanda da aka tsige daga mukamansu, inda aka salame shi daga mukamin babban sakataren jam'iyyar Sudan People's Liberation Movement, wato SPLM a takaice. Kana za a yi masa bincike sakamakon laifinsa na kasa gudanar da harkokin jam'iyyar.

Kafin hakan, jita-jitar da ake yayata wa game da gwagwarmayar neman iko a tsakanin shugaba Kiir da mataimakinsa Machar ta bazu a dukkan kasar Sudan ta kudu. Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, shugaba Kiir ya dauki wannan mataki ba zato ba tsamani sakamakon kokawar neman iko da ke tsakaninsa da sauran manyan shugabannin kasar a karkashin jagorancin Machar.

A hakika dai, tun daga watan Aflilu na bana, shugaba Kiir ya rage sassan iko a hannun mataimakinsa Machar. Daga baya kuma, yayin da yake zantawa da 'wakilin jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya, Machar ya yi bayyani a fili cewa, lokaci ya yi da Kiir ya sauka daga kujerar mulkin kasar. Kana ya bayyana cewa, zai shiga zaben shugaban kasar na shekarar 2015.

Tun bayan da kasar Sudan ta kudu ta samu 'yancin kanta daga Sudan a shekarar 2011, kasar da ta ke dogara ga fitar da mai wajen samun kudin shigar gwamnati tana fama da matsalar tattalin arziki. Ban da wannan kuma, rikicin yankin kasa dake tsakaninta da Sudan da har yanzu ba a daidaita ba, da matsalolin da aka samu a kasar, ciki har da cin hanci da rashawa, sun sanya kasar ta shiga wani mawuyacin hali a cikin gida da waje. Wannan ya sa wasu jami'an kasar suka suka nuna rashin jin dadi kan yadda shugaba Kiir yake tafiyar da mulkin kasar.

Manazarta suna ganin cewa, wannan mataki da Kiir ya dauka na daya daga cikin matakan da ya dauka da nufin murkushe abokan hammaya, tare kuma da kara karfinsa na rike jam'iyyar SPLM.

Abin lura a nan shi ne, kasar Sudan ta kudu kasa ce dake da yawan kabilu da al'ummomi, abin da ya sa kasar ke cikin wani halin siyasa na musamman da kowace kabila ke kokarin nuna tasirinta. Shugaba Kiir ya fito ne daga kalibar Dinka, wadda ta fi girma a kasar, amma mataimakinsa Machar 'dan kalibar Nuer ne wato kabila ta biyu mafi girma a kasar. Kabilar Nuer ta dade tana nuna rashin gamsuwa da matsayin da kabilar Dinka ta dauka a cikin al'umma da harkokin tattalin arzikin kasar.

Ya zuwa yanzu, ko da yake matakin da shugaba Kiir ya dauka na sake kafa majalisar ministoci bai haifar da rikici mai tsanani ba a kasar, amma ya jawo hankalin kasashen duniya sosai, har ma hukumomin MDD dake kasar, da kungiyoyin agaji na kasashen waje dake kasar sun rufe ofishinsu a kasar.

Manazarta suna ganin cewa, idan ba a dauki matakan da suka dace ba, matakin rushe majalisar ministoci zai iya jawo baraka ga jam'iyyar SPLM, abin da ka iya kaiwa ga kawo tashin hankali a kasar, a waje guda kuma watakila za a kara samun rarrabuwar kawuna tsakanin kalibu daban daban na kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China