131122SudantakuduAmi.m4a
|
Kwanan baya wakiliyar musamman ta babban Magatakardar MDD mai kula da harkokin kasar ta Sudan ta kudu, kuma jami'ar dake kula da tawagar musamman ta MDD akan harkokin Sudan ta kudu Madam Hilde F. Johnson ta gabatarwa kwamitin sulhu na MDD bayani game da halin da Sudan ta kudu ke ciki da kuma ayyukan tagawar, inda ta bayyana cewa, ko da yake Sudan ta kudu ta sami dan ci gaba wajen kara karfin raya kasa da dai sauran fannoni, amma, tana fuskantar kalubaloli a wasu manyan fannoni ciki hadda martabar gwamnati, rikicin dake tsakanin al'umma da kuma hana runudar tsaro cin zarafin jama'a da sauransu.
A cewar Madam Johnson, Sudan ta kudu na ci gaba da fuskantar mawuyacin hali, ana cigaba da samun tashe tashen hankula a wasu wurare ciki hadda jihar Jongley, sai dai daga cikinsu rikici a tsakanin kabilar Murle da kabilar Lou Nuer ya zama babbar matsala dake kawo illa ga zaman karko a Sudan ta kudu. Tun daga karshen shekarar 2012, wadannan kabilu suka rika fada tsakaninsu, rikicin da ya auku a watan Fabrairu na shekarar 2013 ya sa mutane fiye da dubu 40 sun yi gudun hijira. Ban da haka, a cikin watanni 6 da ya gabata, an yi ayyuka har 67 wadanda suka sabawa yarjejeniyar tabbatar da matsayin runduna, ciki hadda kawo barzana, kai hari, kama ma'aikatan MDD da sauransu.
Ta yi bayanin cewar bayan sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin arewa da kudu a shekarar 2005, wasu kabilu da kungiyoyin siyasa a kudu sun hada kansu. Amma, akwai bambanci sosai tsakanin wadannan kabilu a fannin al'adu, siyasa, tattalin arziki da sauransu, abin da ya sa aka samu barkewar rikicin siyasa bayan samun 'yancin kan Sudan ta kudu a watan Yuli na shekarar 2011.
Tun waccan lokaci, wasu matsaloli suka rika bullowa a cikin kasar, saboda ganin yadda aka tada rikici, kuma rundunar sa kai da sojoji su kan canja sheka. A sa'i daya kuma, koma bayan tattalin arzikin kasar na jawo damuwar mutane da dama, har ana shakkun cewa, ko Sudan ta kudu za ta iya raya kasa yadda ya kamata kuwa? wadannan abubuwa na da alaka da samun zaman karko da bunkasuwa a kasar Sudan ta kudu, har ma da alaka da ko ya dace ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan ko a'a. Ban da haka, yadda Sudan ta kudu ta daidaita dangantakar dake tsakaninta da makwaciyarta kasar Sudan, ya kasance muhimmin abu ne da Sudan ta kudu ke fuskanta.
Wani mai nazari ya yi nuni da cewa, an samu yamutsattsen hali wajen samun zaman karko da bunkasuwa bayan Sudan ta kudu ta samu 'yancin kai. Wadda ba ta da isashen karfi wajen raya kasa, wato ta kasa samun manufofin kasa da tsarin tattalin arziki bai daya, kabilu ba su nuna cikakken biyayya ga kasar ba, da kuma rashin samun amincewa ga kafuwar wannan sabuwar kasa da sauransu. Yawancin 'yan kasar Sudan ta kudu na kaunar kabilarsu ta kansu.
Game da wadannan matsaloli, ya kamata, gwamnatin Sudan ta kudu ta dauki matakan da suka dace, da ba da jagoranci yadda ya kamata, da kuma fara aikin shimfida zaman lafiya a duk fadin kasar, kada a rika fadan a tsakanin kabilu tare da warware wannan batu yadda ya kamata, sannan a kula da batun raya siyasa a dimokuradiyyance. Ba ma kawai, gwamanti ta dauki nauyin dake wuyanta na kafa wani tsarin siyasar kasa da ya dace ba, har ma ta dauki nauyin kafa wata kawancen kabilu daban-daban mai kyau, ta yadda za ta samu amincewa da goyon baya daga jama'a, domin hakan zai taimaka wajen kafa tunanin 'yan kasar Sudan ta kudu. Wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da zaman karko a fannin siyasa da bunkasuwar tattalin arziki a kasar. (Amina)