in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gabatar da shawarwari guda hudu a dandalin tattaunawa kan batun zaman lafiyar duniya karo na biyu
2013-06-28 15:39:28 cri

An gudanar da dandalin tattaunawa kan batun zaman lafiyar duniya karo na biyu, a ran 27 ga wata a nan birnin Beijing, inda shugabanni da masana kimanin dari daga kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa sama da 60, suka halarci taron da aka yi a jami'ar Tsinghua, domim tattauna kan yadda za a sarrafa kalubaloli a fannin tsaron duniya bisa sabbin hanyoyin da suka dace.

Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya halarci bikin bude taron da aka yi a safiyar wannan rana, inda ya gabatar da sabbin shawarwari guda hudu kan tabbatar da tsaron duniya. Wannan dandali ya kasance na farko da kungiyar mai zaman kanta ta kasar Sin ta aiwatar, wanda ya jawo hankalin kasa da kasa. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2012, ba ma kawai shahararrun masana a wannan fanni suke sa ido kan shi, har ma taron ya janyo manyan shugabannin kasa da kasa.

Yayin da aka gudanar da dandalin na farko a bara, Mr Xi Jinping wanda a lokacin ya kasance mataimakin shugaban kasar Sin ya gabatar da wasu ra'ayoyi, wadanda a ganin masanan ketare, suka bayyana hanyoyin da Sin za ta bi nan da shekaru goma masu zuwa ta fuskar diplomasiyya.

Dandalin a wannan karo yana da jigo "Manyan abubuwa uku dangane da tsaron duniya bisa sauyin halin da ake ciki, wato zaman lafiya, bunkasuwa da kirkire-kirkire". Jami'ar Tsinghua wadda ta dauki nauyin shirya taron ta nuna cewa, dandalin ya mai da hankali sosai kan yadda za a yi hadin gwiwa wajen shawo kan rikice-rikice dangane da batun tsaro.

A cikin jawabin da ya yi a bikin bude taron, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya ce, ya kamata a kafa wani sabon ra'ayi na samar da tsaro bisa tushen tabbatar da samun zaman lafiya, bunkasuwa, yin hadin gwiwa da kawo moriyar juna. Ya ce

"A kasashen yamma, akwai wani karin magana, dake cewa, idan kayayyaki ba su iya ketare kan iyakar kasa da kasa, to sojoji za su ketare. A halin yanzu, za a iya shawo kan rikice-rikice a fannin tsaro ne, idan kasa da kasa sun dinga cudanya da juna tare da tabbatar da ci gaban juna.

A ganin kasar Sin, ya kamata mu yi watsi da tsohon ra'ayin yin takara da juna, sa'annan a nace kan matsayin yin hadin kai da kawo moriyar juna ta yadda za a daidaita matsalar tsaro ta kasa da kasa yadda ya kamata."

A Shekarun baya, rikicin da ya bullo tsakanin Sin da wasu kasashe makwabtanta kan batun tsibirin Diaoyu, tekun kudancin kasar Sin da sauransu, ya jawo hankalin kasa da kasa. A cikin jawabinsa, Li Yuanchao ya nanata matsayin da Sin take dauka na bin manufar zaman lafiya da kasashen waje. Game da yadda za a daidaita wadannan rigingimu, ya ce,

"Sin na mai da aikin samun zaman lafiya matsayin aiki dake kan gaba ta fuskar diplomasiyya. Ya kamata, bangarori daban-daban su nuna hakuri kan wasu matsalolin da aka samo asalin daga tarihi, da kuma warware wadannan matsaloli ta hanyar yin shawarari da sulhu, Sa'anan a daidaita sabanin da ake fuskanta ta hanyar yin shawarwari. "

Ban da haka, taron ya kuma mai da muhimmanci kan harkar tsaro a wasu matsaikata da kuma kananan kasashe. Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya nuna cewa, a yayin dunkulewar kasa da kasa, matsalar tsaro a ko wane yanki za ta kawo cikas ga zaman lafiyar duniya gaba daya. Yayin da ake mai da hankali kan matsalar tsaron kasashe masu tasowa, ya kamata, a dora muhimmanci kan matsalar tsaro a sanadin wasu kasashe masu wadata. Ya ce,

"A kan dauki kasashen masu tasowa matsayin makarfafa na ta'addanci. Amma abin lura shi ne, ayyukan da wasu kungiyoyi na kasashe masu wadata suka yi ke kawo illa ga tsaron duniya."

An ba da labari cewa, za a kwashe kwanaki biyu ana yin wannan taro. Inda mahalarta taro za a tattauna kan wasu manyan batutuwa 4 ciki hadda halin da duniya ke ciki kan batun tsaro, dangantakar dake tsakanin yin kirkire-kirkire da samun tsaron duniya, yin hadin gwiwa ga samun tsaron duniya, da kuma alaka tsakanin samun bunkasuwar zaman al'umma da tsaron duniya.

Ban da haka, a yayin taron, za a tattaunawa kan wasu kananan batutuwa 18 da suka kunshi dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka dangane da batun tsaro, tsaron yankin Asiya-Pacific, tsaron Intanet da hadin kan kasa da kasa, da kuma hana yaduwar makaman nukiliya da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China