A ranar Litinin ne kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki daga shiyyar da kuma bangaren kasa da kasa, da su bullo da matakan da suka dace don magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR).
Kwamishinan kungiyar AU mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Ramtane Lamamra ne ya yi wannan kiran yayin bude taron kungiyar tuntuba ta kasa da kasa game da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da aka yi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Kwamishinan ya ce, ganawar ta nuna irin ci gaban kokarin da gwamnatoci da kungiyoyi ke yi na magance rikicin kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya baki daya.
Shi ma Taye Brook Zerihoun, mataimakin babban sakataren MDD, ya lura da cewa, yanayin da ake ciki a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, batu ne da ke damun majalisar, don haka ya ce, wajibi ne a yi amfani da wannan dama da kungiyar tuntubar ta samar, don cimma matsayar da ta dace tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki don samar da dauwamammen zaman lafiya a kasar. (Ibrahim)