in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'amura sun fara daidaita a CAR
2013-12-09 10:12:30 cri

Rahotanni daga Bangui, babban birnin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR na nuni da cewa, al'amura sun fara daidaita, bayan da kwamitin sulhu na MDD ya amince da tura dakarun kasashen Faransa da Afirka zuwa kasar don maido da doka da oda.

An ga jama'a sun fito kan titunan birnin na Bangui, yayin da dakarun kasar ta Faransa ke sintiri a cikin motoci masu sulke, sai dai kakakin sojojin Faransa Gilles Jarron, ya tabbatar da kashe 'yan tawaye da dama wadanda suka bude wa sojojin Faransa da aka tura filin saukar jiragen sama da ke Bangui wuta ranar Alhamis da safe.

Kimanin mutane 400 ne suka mutu a arangawar da aka yi a wannan makon tsakanin mayakan Seleka da masu goyon bayan tsohon shugaba Francois Bozize, lamarin da ya tilastawa dakarun kasar ta Faransa daukar mataki a ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, a watan Maris ne shugaban rikon kwaryar kasar Michel Djotodia, kana jagoran kungiyar Seleka, ya sanar da zaman makoki na kasa na kwanaki 3 a ranar Asabar, kana ya umarci mayakansa da su koma barikokinsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China