in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da ECCAS na tattaunawa kan shirin kafa sabuwar tawagar wanzar da zaman lafiya a CAR
2013-09-05 15:47:08 cri

Kungiyar AU da ta habaka tattalin arzikin yankin Afirka ta tsakiya ko ECCAS a takaice, na ci gaba da shirye-shiryen kaddamar da sabuwar tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR, tawagar da ake fatan za ta maye gurbin rundunar MICOPAX a kasar.

Wata sanarwar bayan taro na yini biyu da aka fitar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, bayan kammalar ganawa tsakanin kwamishinan kungiyar AU mai lura da harkokin tsaro da wanzar da zaman lafiya Ramtane Lamamra, da babban sakataren kungiyar ECCAS Allam- Mi, ta bayyana cewa, ganawar ta wannan karo na da nufin zartas da kudirin kwamitin tsaron kungiyar AU, da aka cimma a watan Yulin da ya gabata, da ma taron kwararru da ya gudana ranar 21 zuwa 22 ga watan Agusta, na maye gurbin rundunar MICOPAX da sabuwar tawagar AFISM-CAR wadda kungiyar AU za ta jagoranta.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyoyin biyu sun daddale batutuwan da suka shafi lokaci, da kuma tsare-tsaren ayyukan sabuwar tawagar ta AFISM-CAR.

Har ila yau, ana fatan ofisoshin AU da na ECCAS, za su dauki nauyin kafa helkwatar sabuwar tawagar, da ma ragowar bangarorin gudanarwarta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China