in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OPCW ta zartas da cikakken shirin lalata makamai masu guba na Syria
2013-11-16 16:38:56 cri
Majalisar gudanarwar kungiya mai yaki da makamai masu guba ko (OPCW) a takaice, ta zartas da cikakken shirin lalata dukkan makamai masu guba na kasar Syria, kafin rabin shekarar 2014 mai zuwa. Babban sakataren kungiyar ta OPCW Ahmet Uzumcu ne ya bayyana hakan a daren ranar Jumma'a 15 ga wata a birnin Hague, ya na mai cewa, wannan shiri na kunshe da wata cikakkiyar taswira ta tabbatar nasarar da aka sanya gaba.

Bisa wannan mataki,  za a yi jigilar makamai masu guba mafiya hadari, daga Syrian kafin karshen wannan shekara da muke ciki, yayin da kuma za a fidda sauran makaman sannu a hankali, a kokarin tabbatar da gudanar aikin cikin hanzari, da tsaro, tare da kammala shi kafin ranar 30 ga watan Yunin badi.

Wata sanarwa daga kungiyar ta OPCW, ta bayyana cewa, Uzumcu, zai bayyana cikakken shirin lalata makaman nukiliyar sauran kasashen duniya nan ba da dadewa ba.

Da yake karin haske don gane da hakan, Uzumcu ya ce zartas da wannan shiri, ya zamo wata manuniya, dake tabbatar da nasarar da gwamnatin Syria ta cimma.

Bugu da kari yayin taron da aka shirya a wannan rana, mai shiga tsakani na musamman na hadaddiyar tawagar, madam Sigrid Kaag, ta bayyana godiya ga dukkanin kasashen da suka ba da taimakonsu ga wannan aiki, ta fannin tattalin arziki, ko a sauran fannoni. Kaag ta kara da cewa, yanzu haka ana hadin gwiwa da wasu bangarori, wadanda za su taka muhimmiyar rawa wajen kammalar wannan aiki yadda ya kamata, tana mai fatan za yi kokari tare da gamayyar kasashen duniya don cimma burin da aka sanya gaba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China