A wannan rana, rundunar sojojin kasar ta gudanar da wani biki don tunawa da ranar cika shekaru 43 da margayi shugaba Hafiz Assad da magoya bayansa suka yi juyin juya hali. Bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillancin labaran kasar ta Syria, an ce, wasu jami'an rundunar sojan kasa sun ba da jawabi yayin bikin, inda suka nuna cewa, nasarorin da sojojin gwamnatin kasa suka cimma wajen yaki da 'yan ta'adda zai taimaka wajen murkushe shirin 'yan ta'adda da shugabansu, a nan gaba, dakarun rundunar sojan za su kawo karshe ga shirin 'yan ta'adda da kuma masu ba da taimako gare su, dangane da farfadowar kasar Yahudawa.
A wannan rana kuma, yayin da ke halartar wani bikin yanke kyallen dake nuna bude taro na hotuna a birnin Damascus, ministan labaran kasar ta Syria ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun nasara wajen yaki da 'yan ta'adda, babu shakka za a kawo karshen wannan rikici. Ya kuma jaddada cewa, ko da za a gamu da matsaloli da dama, jama'ar kasa zu su farfado da kasa cikin hadin gwiwa.
Kana, bisa labarin da aka samu daga kungiyar adawa ta kasa, an ce, halin yanzu, a birnin Damascus da kuma yankunan dake kewayensa, ana ci gaba da kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati, kungiyar adawa da kuma dakarun kungiyar 'yan ta'adda, kuma sojojin gwamnati na ci gaba da lugudan boma-bomai a yankunan da ke cikin hannun kungiyar adawa. Kwanan baya, jama'a sama da dubu daya dake birnin Damascus da kuma yankunan kewayansa sun gudu zuwa Lebanon. (Maryam)