in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan gwamnatin Syria ta sanar da mamaye garin Hogera dake karkarar Damascus
2013-11-14 12:33:51 cri
Jiya Laraba 13 ga wata ne, rundunar sojan gwamnatin kasar Syria ta sanar da mamaye garin Hogera, wani muhimmin garin dake karkarar birnin Damascus. Lamarin ya sa yake-yaken da ake yi a birnin Damascus da yankunan dake kusa da shi sun shiga wani sabon yanayi.

Bisa labarin da aka samu, an ce, sojojin gwamnati da mayaka fararen hula na yankin sun kwashe tsawon kwanaki shida suna artabu, inda sojojin gwamnatin suka cafke 'yan ta'adda fiye da goma tare da tone abubuwan fashewa da suka binne a kewayen garin. Kuma a halin yanzu, sojojin gwamnatin na kokarin zakulo sauran 'yan ta'adda dake kusa da yankin.

Garin Hajjira ya taba kasance sansanin kungiyoyi masu adawa da gwamnati da 'yan ta'adda, wanda ya ke kusa da babban birnin kasar, kuma wurin da ya hada yankin Subaina wanda kwanan baya sojojin gwamnati suka kwace da sansanin 'yan gudun hijira na Yarmouk wanda a halin yanzu ke hannun 'yan tawaye da sauran wurare. Bugu da kari, manazarta suna ganin cewa, bayan da sojojin gwamnati suka yi nasarar kwace yankunan Hajjira da Subaina, karfin ikon 'yan adawa a kudancin karkarar birnin Damascus ya ragu sosai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China