Wata majiya daga kamfanin dillancin labarai na kasar Najeriya wato NAN ta shaida cewa, an yi zaben cikin doka da oda a jihar ta Enugu, duk cewa masu kada kuri'a ba su fito da dama ba a wasu rumfunan zabe.
A wasu kananan hukumomin dake yankunan kudanci, gabashi gami da yammacin jihar Enugu, an samu mutane masu tarin yawa, musamman ma mata, wadanda suka fito sosai suka jefa kuri'unsu lami lafiya. Amma a wasu kananan hukumomin dake arewacin jihar, kamar su Awgu, Udi, Oji River, da kuma Nsukka, mutane kalilan ne suka nuna sha'awar jefa kuri'a, dalilin tsayawa gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Rahotanni sun kuma kara da cewa, 'yan sanda da masu kiyaye doka da oda sun yi sintiri da zura ido kan masu kada kuri'a a mazabu daban-daban na jihar Enugu.
A zaben wannan karo, 'yan takara sun fafata domin dare kujerun shugabannin kananan hukumomi 17 da na kansiloli 260. Kuma wannan shi ne karo na hudu da aka yi zaben kananan hukumomi bayan da Sullivan Chime ya zama gwamnan jihar Enugu a shekara ta 2007.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.