131029murtala2
|
Shugaban tarayyar Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan, wanda a yanzu haka yake ziyara a kasar Isra'ila, ya nemi taimako da hadin-kan gwamnatin Isra'ila ta fuskar murkushe ayyukan ta'addanci, wadanda ke addabar kasashen biyu a halin yanzu.
Shugaba Goodluck Jonathan yayi wannan furuci ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar ta Isra'ila Shimon Peres a jiya Litinin a birnin Kudus, a ci gaba da aikin ibada irin ta addinin Kirista da yake gudanarwa a kasar.
Jonathan yace, Najeriya na maraba da ganin ingantar hadin-gwiwa da tallafawa juna da Isra'ila, musamman ma a fannin kawo karshen hare-haren ta'addanci, wadanda ke ciwa jama'a tuwo a kwarya a wasu sassan Najeriya.
'ina neman taimakonku da hadin-kan kasar Isra'ila, wajen dakile tabarbarewar yanayin tsaron da muke ciki, babu tantama Isra'ila tana da kwarewa sosai tsawon shekaru, a wannan fage na yaki da 'yan ta'adda, don haka Najeriya zata iya amfana daga wannan kwarewa.' A cewar shugaba Goodluck Jonathan.
Har wa yau kuma, Jonathan ya jinjinawa irin bunkasar alakar tattalin arziki, da kasuwanci tsakanin Najeriya da Isra'ila, ya kuma yi kira da a fadada hadin-gwiwa a ragowar sauran fannoni.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.