Mr Hong Lei ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron manema labarai, inda ya bayyana rashin jin dadinsa matuka game da gazawar kwamitin sulhun na gabatar da wani kuduri game da jinkirta shari'ar da kotun ICC ke yiwa shugabannin biyu.
Hong ya ce, kasar Sin ta yi imanin dewa, batutuwan da suka shafi zaman lafiya da kwanciyar hankalin nahiyar Afirka, kamata ya yi kwamitin sulhu ya saurare su da idon basira kana ya gabatar da wani kuduri da zai dace da muradun AU da sauran kasashen Afirka.
Kasar Sin tana goyon bayan matakin da kasashen Afirka suka dauka kana ta kada kuri'ar amincewa da wannan kuduri, yana mai cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da suke yi na samo bakin zaren warware wannan matsala. (Ibrahim)