Ya zuwa ranar Litinin 9 ga watan nan, kimanin manyan shugabanni da wakilan kasashe su 91 ne suka bayyana aniyarsu, ta halartar bikin tunawa na musamman ga tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.
Cikin manyan bakin da ake fatan za su halarci wannan bikin tunawa da aka shirya gudanarwa a Talatar nan a babban filin wasa na FNB dake birnin Johannesburg, hadda sarakuna da shuwagabannin kasashe, da wakilan kungiyar tarayyar Turai da na AU, da na kungiyar kasashe renon Ingila da kuma na bankin duniya.
A cewar Mr. Collins Chabane, minista a fadar gwamnatin kasar Afirka ta Kudun, bisa tsarin jana'izar tsohon shugaban kasar, shugaba Jacob Zuma zai gabatar da jawabi ga mahalarta bikin tunawar. Za kuma a ajiye gawar Mandela a wani ginin hukumar kasar dake birnin Pretoria tsahon kwanaki uku masu zuwa. Ana kuma sa ran hakan ya baiwa mahalarta bikin binne gawar damar yin ban kwana da ita tsakanin wadannan kwanaki.
Bugu da kari, a ranar Lahadi mai zuwa ne kuma ake sa ran gudanar da karin addu'o'i ga mamacin a mahaifarsa, wato kauyen Qunu dake gabashin Cape, inda kuma ake fatan binne shi. (Saminu)