in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar ya tashi zuwa Afrika ta Kudu domin halarta bukukuwan jana'izar Mandela
2013-12-10 10:07:50 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya tashi daga birnin Yamai a ranar Litinin da safe zuwa kasar Afrika ta Kudu, a ranar yau Talata zai halarci bikin girmamawa ga Nelson Mandela wanda Allah ya yi masa rasuwa a ranar 5 ga watan Disamban da ta gabata.

Shugaban kasar na Nijar ya samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar, musamman ma shugaban kwamitin kasa na raya tattalin arziki, al'umma da al'adu (CESOC), malam Moussa Moumouni Djarmakoye.

Domin nuna alhininsa game da mutuwar Mandela, shugaba Issoufou ya sanya hannu kan wani kudurin zaman makoki na kwanaki uku a dukkan fadin kasar Nijar.

A cikin sakon da ya aika ga takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, shugaban kasar Nijar ya bayyana cewa, mutuwar Mandela ta kasance wani babban rashi ne ga nahiyar Afrika, saboda shi ne babban jarumi da ya yi gwagwarmaya domin tabbatar da tsarin demokaradiyya, mutum mai hangen nesa kan siyasa da imani, ayyukan da ya yi da za su kasance abin koyi da sheda ga nahiyar Afrika da ma duniya baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China