Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta sanar a ranar 8 ga wata cewa, ya zuwa yanzu shugabannin kasashe 28 sun tabbatar da halartar bikin jana'izar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.
Ministan da ke kula da harkokin fadar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu Mista Collins Chabane ya bayyana a ran nan cewa, shugabannin da za su halarci bikin jana'izar Mandela sun zo daga kasashe 13 na Afirka da kuma 15 daga sauran kasashen duniya. Haka kuma akwai shugabannin da suka fito daga kungiyoyin duniya da shiyya-shiyya da suka hada da MDD, da hukumar kungiyar tarayyar Turai, da kungiyar tarayyar Afirka da dai sauransu.
Collins ya nuna cewa, shugabannin da suka tabbatar da halarci bikin sun hada da shugaban kasar Amurka Barack Obama, da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff.
Ban da wannan kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Hong Lei ya sanar a ran 8 ga wata cewa, daga ranar 9 zuwa 11 ga wata, a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin, mataimakin shugaban kasar Li Yuanchao zai je kasar Afirka ta kudu domin halartar bikin jana'izar Mandela.(Danladi)