Kungiyar tarayyar Afrika AU, jakadan kasar Afrika ta Kudu da gwamnatin kasar Habasha sun gudanar da bikin tunawa da Nelson Mandela a cibiyar kungiyar AU dake Addis Abeba, babban birnin Habasha.
A karkashin jagorancin mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU kuma tsohon jakadan kasar Afrika ta Kudu, Erastus Mwencha, an fara bikin tunawar da addu'o'in addinai daban daban. Haka kuma an watsa bidiyo da wake-wake bisa rayuwar Mandela da abubuwan alherin da ya kawo wa duniya a yayin wannan biki, wanda ya samu halartar manyan jami'an kungiyar AU, gwamnatin kasar Habasha da jami'an diplomasiyya na kasashen waje.
Jakadan kasar Afrika ta Kudu dake kasar Habasha da AU, mista Ndumiso Ntshinga ya gabatar da wani jawabi mai sosa rai game da rayuwar Mandela.
A nata bangare, madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, ta jinjinawa kokarin da Mandela ya yi domin 'yancin bil adama da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a nahiyar Afrika.
Faraministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn, kuma shugaban kungiyar AU a wannan karo ya bayyana cewa, Nelson Mandela na daya daga cikin manyan 'yayan Afrika kuma shi ne gwarzon da ya kawo babbar gudummawa ta musamman ga duniya. (Maman Ada)