Za a shirya taron tattaunawa, da yin jawabi da ba da shawarwari da sauran hanyoyi don gudanar da aikin fadakar da jama'a wajen kiyaye ikon mallakar fasaha a tsawon makon da aka kebe na bana.
Mataimakin direkta na ofishin hukumar kula da kiyaye ikon mallakar fasaha na Sin Han Xiucheng ya bayyana cewa, yana fatan kara kokarin fadakar da jama'a wajen kiyaye ikon mallakar fasaha don taka rawar da ta dace wajen daidaita sana'o'i, da canja salon raya tattalin arziki, da kyautata fasahohi da yin gyare-gyare game da masana'antu, da daukar hakikanin matakai wajen fadakar da jama'a don karfafa tunaninsu wajen kiyaye ikon mallakar fasaha, da kyautata yanayi a zamantakewar al'umma da inganta kwarewar jama'a wajen yin kirkire-kirkire, kana kuma, za a kokarta wajen mayar da akidar girmama ilmi, da samar da kirkire-kirkire da bin doka cikin sahihanci don ya zama tunanin jama'a, wannan zai taimaka wajen kara kawo muhalli mai kyau wajen gina kasa ta hanyar bunkasa kirkire-kirkire.(Bako)