in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar kasar Sin na rika kara sani kan ikon mallakar fasaha
2012-04-18 16:48:13 cri

Ranar 26 ga watan Afrilu na kowace shekara rana ce ta kiyaye ikon mallakar fasaha, kasar Sin ta shirya jerin shagulgula don bikin makon kiyaye ikon mallakar fasaha daga ran 20 zuwa ran 26 ga wannan wata. A shekarun baya, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan kare ikon mallakar fasaha da kuma fadakar da jama'a game da shirin, a sakamakon haka, jama'ar kasar Sin na kara fahimtar muhimmancin wannan iko.

Taken bikin na bana shi ne "kwararru a fannin kirkiro sabbin kayayyaki". A shekarar 2000, kasar Sin da kasar Algeria sun ba da shawara ga kungiyar kula da harkokin kikaye ikon mallakar fasaha ta duniya don tsai da ranar kiyaye ikon mallakar fasaha. Gwamnatin kasar Sin da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na kasar su kan fadakar da jama'a game da kiyaye ikon mallakar fasaha a kowace shekara, a sakamakon haka, jama'ar kasar suna kara fahimtar wannan shiri. Mataimakin darektan hukumar kula da harkokin ikon mallakar fasaha ta kasar Sin Han Xiucheng ya ce,

"Ana fatan jama'ar kasar Sin za su girmama fasaha da kara sa himma wajen kirkiro sabbin kayayyaki bisa sonsu, domin kafa tsarin zaman al'umma mai inganci."

Manufar fadakar da jama'a game da kiyaye ikon mallakar fasaha ta yi tasiri sosai ga zaman al'ummar Sin, wannan ya sa, an kara fahimtar matsalolin kare ikon mallakar fasaha a fannonin kimiyya da kasuwanci da al'adu da kuma fina-finai. Bisa kididdigar da babbar kotun kasar Sin ta bayar, a shekarar 2011, yawan laifuffukan da suka shafe keta ikon mallakar fasaha da kotunan wurare daban daban na kasar Sin suka kula da su ya karu da kashi 40 cikin dari. Kana yawan matsalolin da suka shafi tamburan kamfannoni da ikon mallakar littattafai shi ma ya karu. Alal misali, a fannin ikon mallakar littattafai, kakakin babbar kotun kasar Sin Sun Jungong ya bayyana cewa,

"Yawan matsalolin karya ikon mallakar littattafai da kotuna daban daban suka karba a shekarar 2011 ya kai 35185, wanda ya karu da kashi 42.34 bisa na shekarar 2010. Bugu da kari, yawan matsalolin da suka shafi karya ikon mallakar fasahar internet ya karu sosai, wanda kuma ya kara jawo hankalin mutane."

A fannin kare ikon mallakar fasaha, jama'ar kasar Sin sun kara fahimtar wannan iko. Sannan hukumomin gwamnatin kasar sun kyautata tsarin shari'u domin kara kare ikon mallakar fasaha. A karshen watan Maris na wannan shekara, an sanar da daftarin dokar ikon mallakar littattafai, wanda ya jawo hankalin mutane sosai.

A game da haka, mataimakiyar 'yan kallo na hukumar ikon mallakar kayayyakin al'adu ta kasar Sin Duan Yuping ta ce,

"A cikin daftarin, mun mayar da martani ga kalubalen da sabbin fasahohi suka haifar, musamman ma a fannin bunkasuwar fasahohin internet, mun sanya ikon habaka labarai a internet a cikin shari'u."

A makon kiyaye ikon mallakar fasaha na wannan shekara, hukumar kula da ikon mallakar kayayyakin al'adu ta kasar Sin za ta yi aikace-aikace ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohi. Ban da haka kuma, hukumomi da dama na gwamnati za su ba da horaswa ko kuma darusa kan dokar ikon mallakar fasaha. Ban da haka kuma, hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin za ta kafa cibiyoyin gwaje-gwaje kan tantance ikon mallakar fasahohi, kana za ta sanar da yanayin bunkasuwar ikon mallakar fasaha da kuma yin bincike kan manyan batutuwa game da wannan aiki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China