Wu Xiaoming ya yi wannan furuci ne yayin da ya halarci wani taro dangane da wannan fanni, inda ya ce, Sin ta gudanar da aikin yaki da kayan jabu da marasa inganci da harkokin karya ikon mallakar fasaha daga watan Oktoba na shekarar 2010 zuwa watan Yuli na shekarar 2011, inda aka samu ci gaba mai kyau. Muhimmin aiki da aka sa gaba shi ne yin kwaskwarima a wasu yankuna da kasuwani da suka fi fama da wannan matsala. Ban da wannan kuma, kara karfi a wannan fanni da tsai da tsarin sa ido wajen kiyaye ikon mallakar fasaha da kyautata dokoki da shari'a a wannan fanni.
Ranar 26 ga wata ya kasance ranar kiyaye ikon mallakar ilim ta kasa da kasa. A wannan rana kuma, hukumar ta kasar Sin ta gabatar da jerin sunayen manyan batutuwa guda 10, manyan matsaloli guda 10 da mutane mafi shahara a wannan fanni guda 10 na shekarar 2011. Ciki har da batun kamfanin Huawei na kasar Sin da ta kai kara a gaban kotu domin zargin karya ikon mallakar fasaha da kamfanin Motorola ya yi, wanda kuma aka samu sulhu tsakaninsu. A ganin wasu masana, abin ya zama abin koyi wajen tabbatar da ikon kamfanonin kasar Sin wadanda suke kasashen ketare.(Amina)