in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kare ikon mallakar ilmi a birnin Lagos na Nijeriya
2012-04-12 14:54:15 cri
A ran 11 ga wata, an bude taron kare ikon mallakar ilmi a Lagos, birni mafi girma a Nijeriya, domin tattauna yadda za a kara kare ikon mallakar ilmi a harkokin shirya fina-finai da bidiyoyi.

Za a shafe kwanaki uku ana yinsa, wato za a gama wannan taron kara wa juna sani a ranar 13 ga wata. A gun bikin bude taron, mai ba da shawara ga hukumar kare ikon mallakar ilmi ta duniya Madam Donnan Hill ta bayyana cewa a gaban mahalartan wannan taro da suka fito daga sassan kasar, sha'anin kare ikon mallakar ilmi yana da muhimmanci ga ko wace kasa, wannan sha'ani ya shafi masana'antu da dama, kuma zai iya ba da taimako wajen samar da aikin yi ga jama'a. Idan babu wannan sha'ani, to, da wuya a cimma burin shirya fina-finai da bidiyoyi da za'a shigar da su kasuwanni da na kuma bukatun jama'a.

Mista Duker, wani babban fordusan fina-finai a tarayyar Nijeriya ya shaida mini cewa, a halin yanzu gwamnatin Nijeriya ta tsara wasu manufofi da dokoki domin kare ikon mallakar ilmi a fannin shirya fina-finai da bidiyoyi. Sai dai wani lokaci a kan kasa awaitar da wadannan manufofi yadda ya kamata dalilin da ya sa wannan matsala ta janyo lalacewar kasuwar fina-finai a Nijeriya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China