Kasar Sin ta fara gabatar da shirin kiyaye ikon mallakar fasaha daga shekarar 2008, a cikin shekaru 3 da suka gabata, an samu sakamako mai kyau wajen gudanar da wannan shiri. Musamman ma a shekarar bara, an samu sakamako mai kyau a fannoni da dama wajen yaki da laifuffukan karya ikon mallakar fasaha, wannan ya sa, jama'ar kasar sun kara sa himma wajen kirkiro sabbin kayayyaki.
Darektan hukumar kiyaye ikon mallakar fasaha ta kasar Sin Tian Lipu ya gabatar da sakamakon da kasar ta samu wajen kiyaye ikon mallakar fasaha a wurare daban daban na kasar a gun taron manema labaru da aka yi a ran 24 ga wata a nan birnin Beijing. Ya ce, yawan batutuwan ikon mallakar fasaha da aka nemi yin rajista ya karu sosai. A shekarar 2011, kasar Sin ta karbi kayayyaki masu tambari da aka yi wa rajista sama da miliyan 1 da dubu 630. Daga cikinsu, yawan sabbin kayayyaki masu inganci da fasaha da aka yi rajista ya kai dubu 690. A sa'in daya kuma, kasar Sin ta kyautata tsarin shari'u domin tabbatar da ikon mallakar fasaha. A yayin da ake yaki da laifuffukan karya ikon mallakar fasaha da kuma kera kayayyakin jabu, an gabatar da laifuffuka sama da 1700 a kotuna. Mr. Tian Lipu ya ce,
"Kiyaye ikon mallakar fasaha shi ne aikin da ya kamata a dade ana yinsa, ba za a kammala shi a cikin gajeren lokaci ba. Gwamnatin kasar Sin ta tsaya kwarai da gaske wajen gudanar da wannan aiki, kuma za ta kafa tsarin shari'u mai inganci domin kiyaye ikon mallakar fasaha. A shekarar bara, mun samu sakamako mai kyau."
Ban da haka kuma, wani batu na daban shi ne bayyana niyyar da gwamnatin kasar Sin ta dauka sosai wajen kiyaye ikon mallakar fasaha, wato kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, ya zuwa shekarar 2015, yawan sabbin kayayyakin da aka kirkiro zai kai 3.3 a tsakanin kowane mutane dubu 10. Mr. Tian Lipu ya ce, yawan jama'ar kasar Sin da suka yi rajistar sabbin kayayyakin da suka kirkiro a bana ya karu bisa kashi fiye da 40 cikin dari in an kwatanta shi da na makamancin lokaci na bara. Hakan ya bayyana cewa, dukkan jama'ar Sin sun sa himma sosai kan kirkiro sabbin kayayyaki. In haka, watakila za taimaka wajen cimma buri na shekarar 2015 a shekara mai zuwa.
Ban da haka kuma, wani jami'in hukumar masana'antu da kasuwanci ta kasar Sin ya ce, yawan tamburan da aka nemi yin rajista a kasar Sin ya karu, amma bai dace da yanayin bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri ba. Kamfannonin kasar Sin ba su raya kansu ta hanyar yin amfani da kafa tamburansu ba. Kuma ya kamata a kara karfinsu wajen shiga kasuwannin duniya.
Ofishin gwajin tamburan kayayyaki na duniya ya bayar da kididdiga a shekarar 2011 cewa, akwai kamfannoni 21 ne kawai daga cikin kamfannoni mafiya karfi 500 na duniya, kana kamfannonin Sin 4 ne kawai suke cikin matsayin kamfannoni 100 dake kan gaba na duniya. Mataimakin darektan hukumar masana'antu da kasuwanci ta kasar Sin Fu Shuangjian ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokarin amfani da tambura da kare su yadda ya kamata. Ya ce,
"Muna kokarin jagorantar kamfannoni wajen amfani da tambura yadda ya kamata domin kara karfin tamburansu. Sannan kuma, muna kokarin nuna goyon baya ga kamfannonin kasar Sin da su fita zuwa waje domin yada sunayensu a duniya."
Wannan jami'i ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yaki da laifin kera kayayyakin jabu da karya ikon mallakar fasaha domin kyautata yanayin kare tambura. Ya ce, kasar Sin za ta kafa tsarin shari'u mai dorewa domin kyautata yanayin kasuwa, ta yadda za ta kiyaye ikon mallakar tambura na kamfannoni na cikin gida da na waje.(Lami)