A ranar Talata, cibiyar kasuwanci ta kungiyar kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma Afirka ta Kudu, ta sha alwashin inganta hadin gwiwa a fannoni da dama.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, cibiyar kasuwanci ta kungiyar BRICS na mai nuna cewa, kasashen biyar masu tasowa a fuskar tattalin arziki za su kara hadin gwiwar bunkasa ababan more rayuwa, harkokin hako ma'adinai, kara darajanta kayayyaki da ake sarrafawa, fasahohi da kuma dorewar bunkasa.
Cibiyar ta baiyana dagewar kasashe mambobin kungiyar a fuskar inganta shirye shiryen kafa bankin bunkasa na BRICS.
An kafa cibiyar kasuwanci ta kungiyar BRICS din ne yayin ganawar kungiyar jiko na biyar da aka yi a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu cikin watan Maris, inda a wannan lokaci ne shugabannin kasashen biyar suka amince a kafa bankin bunkasa don samar da kudaden ayyukansu na ababan more rayuwa. (Lami)