in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu tana shirin kiran taron shugabannin kungiyoyin hadin gwiwwa na BRICS
2013-10-22 10:32:18 cri

Hukumar hadin gwiwwar koli ta kasar Afrika ta Kudu SANACO a ranar Litinin din nan ta shirya taron kara wa juna sani a birnin Johannesburg tare da kungiyoyin hadin gwiwwa na kasashen BRICS.

Taron na shugabannin kungiyoyin hadin gwiwwa na kasashen BRICS dai, sashen ciniki da masana'antu da hadin gwiwwa tare da hukumar koli ta kungiyoyin hadin kai ta kasar Afrika ta Kudu SANACO ne za su dauki nauyin shirya shi a ranar 26 zuwa 27 na wannan watan na Oktoba a birnin Cape Town.

Shi dai sunan BRICS yana wakiltar kasashe masu tasowa ne guda biyar wato Brazil, Rasha, India, Sin da Afrika ta Kudu.

Shugaban ita hukumar hadin gwiwwar ta SANACO Lawrence Bale ya yi bayanin cewar, za'a kira taron ne domin a tattauna yadda za'a inganta dangantakar hadin gwiwwa da fahimtar juna a tsakanin kungiyoyin hadin gwiwwa na wadannan kasashe biyar.

Taron da za'a yi shi karkashin taken hada hannu domin cigaba, cudanya da samar da masana'antu ta hanyar aiki tare, zai kawo shugabannin kungiyoyin wadannan kasashe biyar wuri daya domin musayar ra'ayi ta bangaren abin da kowannen su ya fuskanta a nashi aikin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China