in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bukaci mambobin BRICS da su kara hada kai
2013-09-06 10:08:49 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada a ranar Alhamis cewa, kamata ya yi mambobin kasashen BRICS su fadada tunaninsu game da batutuwan da suka shafi kasa da kasa da karfafa dangantaka da hadin gwiwa.

Shugaba ya yi wadannan kalamai ne a taron shugabannin kungiyar kasashen BRICS wanda ya kunshi kasashen Brazil, Russia, India, Sin da kuma Afirka ta Kudu, gabanin taron kolin G20 da za a yi a birnin St. Petersburg na Russia.

Ya ce, bisa yanayin da ake ciki yanzu a duniya, kamata ya yi kasashen na BRICS su shiga a dama da su wajen warware tasirin da manufofin kudi marasa nagarta na kasashe masu ci gaban tattalin arziki suka haifar.

Bugu da kari shugaban na Sin, ya ce, kamata ya yi mambobin na BRICS su hada kai wajen kare tare da bunkasa tattalin arzikin duniya cikin adalci, adawa da kariyar cinikayya, kiyaye tsarin cinikayya tsakanin kasashe da ciyar da zagayen tattaunawar cinikayya ta Doha gaba. Sannan ya ce, akwai bukatar a hanzarta kokarin da ake na kafa wata cibiyar kiyaye manufofin kudin kungiyar.

Sauran shugabannin da ke halartar taron, sun bayyana cewa, har yanzu tattalin arzikin duniya yana fuskantar hadari da kalubaloli, da kuma tarnaki wajen farfadowa.

Don haka, sun bukaci manyan kasashe masu ci gaban tattalin arziki, ciki har da kungiyar G20, da su rika daidaita manufofinsu na tattalin arzikin kasa, kana su hada gwiwa wajen samar wa tare da bunkasa tattalin arzikin duniya mai dorewa cikin daidaito.

Tun da farko a wannan rana, mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao, ya ce, kasashen BRICS sun amince da a samar da wata gidauniyar hadin gwiwar ajiyar kudaden ketare ta dala biliyan 100.

Wannan yunkuri ya zo ne bayan da kasashen suka amince yayin taron kolin kungiyar na wannan shekara da aka yi a Durban na kasar Afirka ta Kudu game da bukatar kafa bankin hadin gwiwa na kungiyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China