Ministocin harkokin waje na kasa da kasa za su shiga shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran
A ranar 22 ga watan nan ne aka sanar da gaza kammala shawarwarin Geneva da ake yi tsakanin kasashe shida da kasar Iran kan batun nukiliyar kasar ta Iran wanda aka gudanar cikin kwanaki uku. Don kawar da bambance-bambance kan wasu muhimman batutuwa, bangarori daban daban da abin ya shafa za su tura manyan jami'ai don ci gaba da yin shawarwarin, inda aka tsawaita lokacin yin shawarwari zuwa kwanaki hudu. A halin yanzu, ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya riga ya isa birnin Geneva, kuma takwaransa na Amurka John Kerry, na Faransa Laurent Fabius da kuma na Ingila William Hague sun tabbatar da aniyarsu ta zuwa birnin na Geneva don shiga shawarwarin.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na kasar Sin Hong Lei ya sanar a ranar 23 ga wata cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya riga ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Geneva don halartar shawarwarin.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Iran IRNA ya bayar a yammacin ranar 22 ga wata, an ce, ministan harkokin waje na Iran kuma babban wakilin kasar a wurin shawarwarin Mohammad Javed Zarif ya bayyana cewa, an samu sakamako kimanin kashi 90 cikin dari na dukkan batutuwan da ake tattaunawa, amma akwai muhimman batutuwa biyu da ake bukatar daidaita su, ya ce ya kamata a ci gaba da tattauna don warware su. (Zainab)