Kasar Sin za ta fadada shirin goyon bayanta ga kungiyoyi hudu na manyan kasashen Afrika masu noman auduga da aka fi sani da C4, kamar yadda jami'an ciniki na bangarorin biyu suka sanar a wani bangaren taron ministoci na hukumar ciniki ta duniya WTO karo na 9 a ranar Talatan nan 3 ga wata.
Kasar Sin tana kara azama wajen habaka kokarin wadannan kasashen da suka hada da Benin, Burkina Faso, Chadi da kuma Mali wajen noma, sarrafa da kuma jigila cikin hadin gwiwwa na masana'antun auduga, in ji ministan kasuwanci na kasar Sin Gao Hucheng lokacin taron manema labarai.
Yarjejeniyar, in ji shi, ta biyo bayan wani shiri na hadin gwiwwa da aka fara a shekarar ta 2011 lokacin taron ministocin hukumar cinikin duniya karo na 8, wanda ya taimaka wa kasashe hudu dake noman audugar da suka samu kashi 15 cikin 100 na cinikin auduga na duniya.
Haka kuma kasar Sin za ta kara yawan gudunmuwar da take bayarwa wajen gina wuraren aiki, sarrafa kayayyaki, samar da horo na fasaha, nazari, da sufuri tare da ba da kwarin gwiwwa wajen ganin kamfanonin kasar da wadannan kasashen sun hada gwiwwa, duk wadannan za'a yi su ne nan da karshen shekara ta 2014, a yadda yarjejeniyar ta nuna.
Ganin cewa, kasashe masu tasowa suna iya samar da taimako na fasasha wani abu ne da ake maraba da shi, in ji babban daraktan hukumar ciniki ta duniya Roberto Azevedo, wanda ya bayyana hadin gwiwwar ta bangaren noman auduga a wani sabon yunkuri na shawarwarin hukumar. (Fatimah)