in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kiran da a kwantar da hankali bayan sanarwar da Koriya ta Arewa ta bayar
2013-03-06 17:05:06 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta fada a ranar Laraba yayin taron manema labarai cewa, kasar Sin na yin kiran da a kwantar da hankali, bayan sanarwar da Pyongyang ta bayar cewa, za ta soke yarjejeniyar da ta kawo karshen yakinta da Koriya ta Kudu.

Madam Hua ta ce wannan yarjejeniya tana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya.

Ta ce kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su kai zuciya nesa, tare da kaucewa daukar duk wani matakin da zai kai ga rura wutar tashin hankali.

Madam Hua ta ce kasar Sin ta dade tana mai imanin cewa, kamata ya yi matakan zaman lafiya su maye gurbin yarjejeniyar da ta kawo karshen yakin, tana mai cewa, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa, su yi aiki tare don cimma nasarar wannan manufa ta hanyar shawarwari, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China