Wani jami'i daga yankin Taiwan ya bayyana cewa, bayan da aka tattauna da dudduba wasikar da Philippines ta kawo, ana iya cewa, Philippines ta nuna bakin ciki tare da neman gafara game da kai hari kan jirgin ruwa na yankin Taiwan, sabo da haka, a iya cewa, Philippines ta mayar da martani kamar yadda yankin Taiwan yake bukata, amma, duk da haka, akwai saura-rina-a-kaba game da ci gaba da tabbatar da sauran batutuwa, musamman ma batun biyan kudin diyya.
Ya bayyana cewa, yankin Taiwan yana fatan gwamnatin Philippines za ta tsara matakai wajen biyan kudin diyya nan take, da yin alkawarin kaucewa sake aukuwar irin wannan lamari. Ya ci gaba da cewa, yankin Taiwan zai ci gaba da inganta tsaron masu kamun kifaye a wadannan wurare, kuma yanzu, ana ci gaba da ba da kariya ga masu kamun kifaye a wurin.(Bako)