in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Faransa sun kwace wassu makamai a Kidal dake yankin arewacin Mali
2013-11-08 09:43:57 cri

Dakarun sojin kasar Faransa dake kasar Mali sun kwace makamai da 'yan tawaye suka bari a yankin Kidal, inda a nan ne wadansu da ake zargin 'yan kungiyar Al-Qaida ne reshen arewacin nahiyar Afrika AQIM suka sace 'yan jaridan nan guda biyu, kuma daga bisani suka kashe su.

Dakarun sojin na Faransa da yanzu aka kara yawansu sakamakon kisan 'yan jaridar nan su biyu, a ranar Laraban nan suka gano kananan bindigogin hannu guda 40, motoci 10, kwamfuta 10 da sauran kayyayakin aiki a Tin-Essako dake gabashin garin Kidal.

Wani jami'in sojin Mali ya yi wa kamfanin dillanci labarai na Xinhua bayanin cewa, tun bayan sace 'yan jaridan nan su biyu na gidan radiyon kasar Faransa aka kuma kashe su, aka kara yawan sojojin Faransa daga 170 zuwa 320 da kuma karin jiragen sama guda biyu, abin da ya ce, ya kawo jinkirin aika sojojin Malin 300 su maye gurbin nada su 167 da aka tilasta wa tsayawa a barikin sojojin kasar dake Kidal yau kusan watanni 4.

A ranar 4 ga watan da muke ciki ne dai sojojin gwamnatin kasar Niger da ke ba da gudummuwa a Malin suka gano wani sansanin horas da 'yan tawayen masu tsattsauren ra'ayin addinin musulunci a yammacin Afrika wato MUJAO a tsakanin Ansongo da Menaka a arewacin Malin, an dai kama mutum daya da ake zargin hannun shi a cikin tafiyar da sansanin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China