Gwamnatin kasar Nijar ta nuna matukar damuwa tare da yin allawadai game kisan Ghislaine Dupont da Claude Verlon, ma'aikatan rediyon kasar Faransa RFI a Kidal a arewacin kasar Mali bayan da aka sace su.
Hukumomin kasar Nijar dake amana da kare dukkan 'yanci, har ma da na 'yancin samar da labarai, sun yi allawadai da wannan kisan da aka yi a kan 'wadannan yan jarida biyu a lokacin da suka gudanar da aikinsu, in ji wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Nijar a ranar Litinin a birnin Yamai.
A cikin wannan lokaci na bakin ciki, gwamnatin Nijar na amfani da wannan dama domin nuna alhininta ga gwamnatin Faransa da al'ummar kasar Faransa, da ma'aikatan RFI da ma iyalan mamatan.
Baya ga haka, sanarwar ta kara jaddada niyyar gwamnatin Nijar ta cigaba da yaki da ta'addanci daga dukkan fannoni.
Kasar Nijar dai ta tura kimamin sojoji 850 zuwa ga arewacin Mali dake makwabtaka da ita domin taimaka wa maido da zaman lafiya a wannan kasa a cikin tawagar MINUSMA. (Maman Ada)