Ministan tsaro cikin gidan kasar Mali, janar Sada Samake ya sanya hannu a ranar Lahadi a Bamako tare da takwaransa na kasar Faransa Manuel Valls da ke ziyarar aiki a wannan kasa tun ranar jiya, kan wata yarjejeniyar da ta shafi karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar tsaro.
Yarjejeniyar ta shafi musammun ma batun horar da jami'an tsaron kasar Mali domin ba su damar yaki da ta'addanci yadda ya kamata.
Haka kuma yarjejeniyar da ke da nasaba da bunkasa hadin gwiwa a fuskar tsaro wani mataki ne na bayyana huldar moriyar juna da ke tsakanin kasashen biyu tun tsawon shekarun da suka wuce, in ji janar Sada Samake.
Minista Samake ya bayyana cewa, aiwatar da wannan yarjejeniya zai karfafa karfin rundunar sojojin kasar sosai a fannin horaswa, yaki da manyan laifuffuka da kuma samun kayayyakin aiki da gine-gine ta fuskar tsaro. (Maman Ada)