Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Talatan nan 5 ga wata ya yi kira da bukatar samar da zaman lafiya da kuma sulhu a kasar Mali dake fama da tashin hankali, inda zangonsa na farko ne a ziyarar aikin da ya fara kaiwa yankin Sahel tare da shugabannin kawo cigaban kasashen duniya.
Shugaban na MDD yana ziyara ne da ta kafa tarihi a yankin na Sahel tare da shugabannin bankin duniya Jim Yong Kim da manyan jami'ai daga kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU da na bankin cigaban Afrika da kuma na tarayyar Turai.
Tun da safiyar wannan rana a Bamako, babban birnin kasar ta Mali, sai da Mr. Ban ya gana da ministocin kasashen yankin na Sahel.
A bayanin da mataimakin kakakinsa Farhan Haq ya yi wa manema labarai, ganawar ta Mr. Ban ta tattauna yadda shugabannin gwamnatocin wadannan kasashen yankin su yi don warware matsalolin da yankin ke fuskanta, yana mai lura da cewa, yankin zai iya kuma zai je gaba muddin aka hada kai. (Fatimah)