Cikin sanarwar, wadda aka fitar jiya Laraba 27 ga wata, Psaki ta bayyana cewa, Mr. Kerry zai gana da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Jerusalem, inda za su tattauna batun nukiliyar kasar Iran, da shawarwarin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falesdinu da dai sauran batutuwa. Sa'an nan zai gana da shugaban al'ummar Falesdinu Mahmoud Abbas a birnin Ramallah, inda za su tattauna kan shawarwarin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falesdinu da dai sauran batutuwa.
Bisa goyon bayan kasar Amurka, Isra'ila da Falesdinu, sun farfado da shawarwarin samar da zaman lafiya dake tsakaninsu a karshen watan Yulin da ya gabata, suna kuma kokarin neman kulla wata yarjejeniya cikin watanni 9. Sai dai shawarwarin da ake yi sun samu tsaiko, sakamakon ci gaba da gina matsugunin Yahudawa da kasar Isra'ila ta sanar za ta yi a wuraren da ba a amince da su ba.
Duk da haka, yayin taron manema labaran da aka yi ran 27 ga wata, Ms. Psaki ta nuna cewa, Isra'ila da Falesdinu na fatan ci gaba da shawarwari tsakaninsu, don cika alkawarin kulla wata yarjejeniya cikin watanni 9. (Maryam)