Asusun yara na MDD UNICEF, ya bukaci gwamnatin rikon kwaryar kasar Afirka ta Tsakiya CAR, da ta gaggauta gudanar da bincike kan zargin da ake yi, na kisan yara kanana a kasar, biyowa bayan barkewar rigingimun baya bayan.
A cewar wakilin asusun na UNICEF a Afirka ta Tsakiyar Souleymane Diabate, akwai bukatar mahukuntan gwamnatin rikon kwarya a kasar su tabbatar jami'an tsaro na biyayya ga dokokin kasa da kasa, ciki hadda kudurorin kwamitin tsaron MDD, da suka tanaji hana shigar da yara kanana aikin soji, tare da haramta duk wani yanayi da zai ba da kafar cin zarafin yara.
Kasar Afirka ta Tsakiya dai ta auka cikin rigingimun siyasa ne, tun bayan da kungiyar Seleka, da gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen kasar suka hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize daga mukaminsa cikin watan Maris da ya gabata.
Bugu da kari, ci gaba da dauki ba dadi tsakankanin bangaori da ba su ga maciji da juna, na kara barazana ga burin wanzar da yanayin zaman lafiya, da maido da salon mulkin dimikaradiyya a kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin al'ummar kasar sama da miliyan 4.6 ne ke fama da matsanancin yanayin rayuwa, baya ga yawaitar kashe-kashen rayuka dake barazana ga zaman lafiyar kasar. (Saminu)