Kakakin MDD Martin Nesirky, ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa, tawagar MDD da ke DRC, kasar jamhuriyar demikoradiyar Congo (MONUSCO), ta taimaka wajen tura 'yan sandan kasar Congo 200 zuwa yankunan da aka kwato daga hannun 'yan tawayen M23.
A cewar wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar ta jamhuriyar demokiradiyar Congo, Martin Kobler, wannan wani bangare ne na aikin tawagar na taimakawa gwamnati wajen maido da harkokin iko.
Tawagar ta MONUSCO ta kuduri aniyar taimakawa wajen jigilar karin jami'an soja 300 daga rundunar kota-kwana zuwa arewacin Kivu. baya ga jami'an soja 900 da za a dauko daga sauran yankuna zuwa Kiwanja, Rutshuru, Rumangabo da sauran yankunan da aka kwato.
Kakakin na MDD ya kuma bayyana cewa, tawagar ta MONUSCO, za ta kafa ofisoshin 'yan sandan MDD a Kiwanja da Masisi a cikin kwanaki masu zuwa don taimakawa ayyukan 'yan sandan kasar.
Ya kuma nanata cewa, aikin tawagar, shi ne ta karya lagon dukkan kungiyoyin dake dauke da makamai ba kawai kungiyar M23 ba, sai dai Kobler ya ce, kamata ya yi wadannan kungiyoyin da ke dauke da makamai su shiga cikin shirin mika mulki na kasar wanda ya bayyana muhimmancin ci gaba da aiwatar da shi.
Idan ba a manta ba, a ranar 5 ga watan Nuwamba ne, kungiyar ta M23 ta ayyana kawo karshen tayar da kayar bayan da ta fara a kasar tun a watan Afrilun shekarar 2012, kuma sojojin Congo sun tabbatar da wannan ci gaba da aka samu.
Sai dai an dakatar da wata yarjejeniyar da ake sa ran sanya hannu a kai a ranar Litinin tsakanin sassan biyu, bayan da jami'an kasar Congo suka bukaci karin lokaci domin su nazarci bayanan. (Ibrahim)