in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin MDD ya bukaci a sulhunta rikicin siyasa da ake fuskanta a DRC
2013-11-08 10:48:58 cri

Ofishin MDD dake kasar jamhuriyar demokradiya ta Kongo DRC a ranar Alhamis din nan 7 ga wata ya yi kiran da a sulhunta rikicin siyasar da ake fuskanta a kasar ta hanyar cigaba da tattauna cikin lumana, kiran da ya zo kwanaki biyu bayan da kungiyar 'yan tawaye ta M23 ta sanar da aje makamai.

Ofishin majalissar na MONUSCO ya tabbatar da cewar, a yanzu haka sojojin kasar Kongo ne ke rike da daukacin wuraren da a da 'yan kungiyar tawayen ke da karfi, in ji Farhan Haq mataimakin kakakin Majalissar a bayanin da ya yi wa manema labarai.

Ya ce, MONUSCO na goyon bayan ayyukan da sojojin gwamnati suka yi na cika alkawarinsu na kare lafiyar al'ummar kasar da kuma hada kan sojojin guri daya.

Shugaban kungiyar M23 Bertrand Bisimwa a ranar Talata ya sanar da cewa, ya shawarci kwamandojinsa da su aje makamai a matsayin wani mataki na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati.

Martin Kobler, babban wakilin MDD a kasar wanda ke jagorantar MONUSCO ya ce, yana da muhimmanci a samu warware rikicin siyasar da ake fuskanta ta hanyar amfani da yarjejeniyar Kampala, yana mai gargadin sauran kungiyoyin 'yan tawayen da kada su ce za su yi amfani da wannan dama da kungiyar M23 ta aje makamai wajen kawo wani rigima domin rundunar MONUSCO dake da alhakin kare lafiyar al'umma ba za ta kyale su ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China