in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan yunkurin warware matsalar siyasa dake addabar DRC
2013-11-07 10:19:38 cri

Shugaban kwamitin tsaron MDD na karba karba, kuma wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kasarsa na matukar goyon bayan duk wani matakin lumana, da zai kai ga warware rikicin siyasar dake addabar jamhuriyar dimikaradiyyar Congo DRC.

Liu Jieyi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, biyowa bayan wani zama da kwamitin tsaron ya gudanar a wannan rana, ya kara da cewa, Sin ta yaba da irin ci gaban da aka samu a gabashin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Kafin tsokacin na Mr. Liu Jieyi a wannan rana, jagoran tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDDr dake jamhuriyar dimokaradiyyar Congo Martin Kobler, da wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a yankin manyan tafkunan Afirka Mary Robinson, sun gabatarwa zauren kwamitin tsaron bayanai, don gane da irin ci gaban da ake samu a wannan kasa, da ma yankin baki daya, tare da karin matakan da ake da bukatar dauka a nan gaba.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai kungiyar 'yan tawayen M23 ta bayyana aniyar aje makamai, tare da kawo karshen tawayen da take yi tun cikin watan Afirilun shekarar bara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China