Cutar Asma, cuta ce data danganci yawan tari cikin dare da daukewar nunfashi da nauyin kirji da canjin nunfashi wanda ke hana iska gudana cikin huhu.
Ana samun cutar Asma ta hanyar wasu kwayoyin cututtuka ko canjin yanayi kamar gurbatacciyar iska, sanyi , kura da dai sauran su.
A yayin da sanyi ke kara kunno kai a wasu jahohin Najeriya ciki harda jihar Kano , yawancin mutanen da suke fama da wannan cuta suna tsintar kansu cikin yanayin wahala sakamakon kurar hazo da iska.
Amina Isma`il tana daga cikin masau dauke da wannan cuta tace tana cin wahala sosai a irin wannan yanayi, domin sau tari sai ta yi amfani da maganin shaka wato Inhaler idan nunfashin ta ya fara daukewa.
Wani kwararren likita a asibitin koyarwa na malam Aminu kano Dr. Bashir Husaini Abdullahi yayi bayanin cewa wajibi ne masu wannan cuta su guji shiga kura ko sanyi, sannan kuma su rinka kiyayewa wajen amfani da wasu tsummuka wadanda suke dauke da kura ko datti.(Garba Abdullahi Bagwai)