in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya na neman kara lokacin dokar-ta-baci a jihohin Yobe, Borno da Adamawa
2013-11-07 10:45:41 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan cikin wasu wasikun da ya aika ga shugabannin majalisun dokokin kasar, ya bukaci da su amince da kudurinsa na kara tsawon lokacin dokar-ta-bacin da aka sanya a jihohin Yobe, da Borno da Adamawa dake arewa maso gabashin kasar, sakamakon yawan tashe-tashen hankula da ake ci gaba da samu a wadannan yankuna.

A watan Mayun wannan shekara ne dai aka sanya dokar-ta-baci a jihohin na tsawon watanni shida, wadda zata kare a wannan wata nan na Nuwamba. Sai dai a yanzu haka, shugaban ya nemi majalisun da su amince ya sake kara tsawon wa'adin dokar har na tsawon watanni shida nan gaba, a cewarsa har yanzu dai akwai barazanar tsaro a wasu sassan jihohin.

Idan majalisun suka amince da kudurin na shugaba Jonathan, sabon wa'adin da aka kara zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan da muke ciki.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga birnin Ikko, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China